1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Shugaban Kamaru ya kara tsaurara matakan tsaronsa

August 5, 2026

Shugaban Kamaru Paul Biya ya yi sabbin nade-naden manyan hafsoshin soji domin kara tsaurara tsaronsa, yayin da ake ci gaba da cece-kuce kan rashin bayyanarsa na dogon lokaci a bainar jama'a.

Shugaban Kamaru, Paul Biya lokacin da yake gabatar da jawabi a Yaounde
Shugaban Kamaru, Paul Biya lokacin da yake gabatar da jawabi a YaoundeHoto: Angel Ngwe/AP Photo/picture alliance

Sabbin nade-naden sun hada da Janar Raymond Jean Charles Beko'o Abondo a matsayin shugaban masu tsaron fadar shugaban kasa, karo na farko da janar ke rike da wannan mukami.

Biya mai shekaru 93, wanda ya shafe kusan watanni biyu ba a gan shi ba, ya kuma nada sabon mataimakin babban hafsan tsaron kasar.

Sai dai gwamnatin Kamaru ta ce lafiyar shugaban ba ta tabarbare ba, kuma zai dawo kasar nan ba da jimawa ba, duk da cewa 'yan adawa na cewa rashin bayyanarsa ya haifar da gibi a shugabancin kasar.