1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAsiya

Shugaban kasar Iran Ebrahim Raisi ya rasu

May 20, 2024

Hukumomin Tehran sun tabbatar da mutuwar shugaban kasar Iran Ebrahim Raisi da dukkan mutanen da ke cikin jirgin shelikwaftar da ya yi hadari da shugaban akan hanyarsa ta dawowa Iran daga Azerbaijan.

Shugaban Iran Ebrahim Raisi ya daga hoton Janar Kassim Soleimani a zauren Majalisar Dinkin Duniya a 2022
Shugaban Iran Ebrahim Raisi ya daga hoton Janar Kassim Soleimani a zauren Majalisar Dinkin Duniya a 2022Hoto: Mary Altaffer/AP/picture alliance

Mataimakin shugaban kasar Mansouri shi ne ya tabbatar da mutuwar shugaban kamar yadda ya wallafa a shafinsa na X. Kazalika dukkan mutane biyar din da ke tare da shugaban sun mutu ciki har da ministan harkokin wajen kasar Hossein Amirabdollahian da gwamnan lardin Azerbaijan na gabashin Iran da kuma wasu jami'ai da ke kare lafiyarsu.

Karin bayani: Batan dabon jirgin da ke dauke da shugaban Iran na firgita al'ummar kasar 

Raisi shi ne shugaban kasar Iran na biyu da ya mutu a kan karagar mulki, baya ga shugabaMohammad Ali Rajai da ya mutu a 1981  sakamakon tashin wata nakiya bayan juyin juya halin Iran.

Karin bayani: An kama wadanda ake zargi da hare-hare a kasar Iran 

Kasashen duniya na ci gaba da nuna alhini kan mutuwar shugaban kasar Iran Ebrahim Raisi wanda ake hasashen shi ne ke kan layi na zama jagoran addinin kasar wato magajin Ayatollah Ali Khamenei.

Tuni dai kungiyar Hamas ta fitar da sanarwar ta'aziyya tare da jaddada goyon baya ga jagoran addinin kasar Ayatollah Ali Khamenei da gwamnati har ma da daukacin al'ummar Iran a wannan lokaci na bakin ciki a fadin kasar.

Karin bayani: Duniya ta bukaci kai zuciya nesa tsakanin Israila da Iran 

Kazalika shugaban mayakan Houth masu gwagwarmaya da makamai Mohammed Ali AL-Houthi, ya wallafa sakon ta'aziyya a shafinsa na X, inda ya ce marigayin ya nuna dattako wajen goyon bayan Falasdinawa tare da zama barazana ga Isra'ila.

Firaiministan Indiya Narendra Modi, a sakon da ya wallafa a shafinsa na X, ya ce ya kadu mataka kan mutuwar Dr. Seyed Ebrahim Raisi, wanda ya bada gudummuwar da ba za a taba mantawa a tarihi ba, kan yaukaka dangantakar Indiya da Iran. Haka lamarin yake a Iraqi inda ma'aikatar harkokin wajen Bagadaza ta aike da sakon ta'aziyya ga daukacin al'ummar Iran.