Shugaban kasar Kenya ya nada sabuwar gwamnati
December 8, 2005Makwani 2 bayan da al´ummar kasar Kenya ta yi watsi da saban kundin tsarin muklkin kasa a zaben raba gardama da a ka yi, shugaban kasa Mwai Kibaki yayi garambawul ga gwamnatin sa.
Jim kadan, bayan bayyana sakamakon zaben ne, ya rusa gwamnatin, sabili da mumunan kayin da ya sha.
A cikin sabuwar gwamnatin ministoci kalilan su ka yi tazarce da su ka hada da ,ministan kudi da na sadarwa aboka sa na kut da kut.
Babu ko daya, daga ministocin da su ka yi neman zaben kin amincewa da kundin, da ya dawo cikin sabuwar gwamnatin.
Wannan mataki da shugaban kasar ya dauka bai ba masharahanta mamaki ba, to saidai da dama, na zargin sa da nuna rashin adalci, domin kamata tayi ,wannan ministoci su dawo, ta la´akari da yadda al´ umma ta basu goya baya, ta hanyar watsi da kundin tsarin mulki.