1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Shugaban Kenya ya nada 'yan adawa a cikin gwamnati

July 24, 2024

Shugaban kasar Kenya William Ruto ya sanar da nadin wasu kusoshin 'yan adawa hudu a cikin sabuwar gwamnatinsa don shawo kan zanga-zanga ta fiye da wata guda da ta barke a kasar tare da yin ajalin mutane da dama.

Kenia Nairobi | William Ruto gewinnt Präsidentschaftswahl
Hoto: TONY KARUMBA/AFP/Getty Images

Wadannan mutane hudu dukanninsu mambobin ne na babbar jam'iyyar adawa ta Orange Democratic Movement ODM ta Raila Odinga wanda a baya ya lashi takobin kawo karshen gwamnatin William Ruto.

Karin bayani: Ruto ya rusa majalisar ministocinsa

Mutanen da aka bai wa manyan mukaman sun hadar da John Mbadi da aka nada a matsayin munistan kudi, da James Opiyo Wandayi shi kuma a matsayin ministan man fetur da makamashi, sai Hassan Ali a mukamin minstan ma'adinan karkashin kasa sai daga karshe Wycliffe Oparanya a mukamain ministan bunkasa manya da matsakaitan masana'antu.

Karin bayani: Ruto ya nada wasu daga cikin sabbin ministoci

Abin jira a gani dai shi ne ko wannnan mataki zai kwantar da boren da ya taso a Kenya wanda ke neman ya kifar zababbar gwamnatin ta William Ruto.