Shugaban Kenya ya rage wa kansa albashi
March 8, 2014Shugaban kasar Kenya Uhuru Kenyatta ya bayyana rage albashinsa da na mataimakinsa William Ruto da kashi 20 cikin 100, yayin da sauran ministoci za a rage albashinsu da kashi 10 cikin 100, kuma matakin ya fara aiki nan take.
A wannan Jumma'a da ta gabata majalisar gudanarwa ta kasar, ta amince da matakin cikin shirin tsuke bakin aljinhun gwamnati, domin neman hanyoyin samar da ci-gaba. Shugaba Kenyatta ya ce ana amfani da kudaden da suka kai dalar Amirka bilyan 4.6, kwatankwacin Euro bilyan 3.3 wajen biyan albashi ma'aikatan gwamnati duk shekara, inda dala bilyan 2.3 kawai ke raguwa wa sauran ayyukan ci-gaba. Shi kansa shugaban yana samun albashin da ya kai dala dubu 13 a duk wata. Shugaban ya nemi 'yan majalisar dokokin kasar domin amincewa da rage musu albashi.
Shugaba Uhuru Kenyatta na kasar ta Kenya, ya bayyana shirin gwamnati na tabbatar da samar da ci-gaba mai dorewa ga kasar mafi karfin tattalin arziki tsakanin kasashen gabashin nahiyar Afirka.
Mawallafi: Suleiman Babayo
Edita: Usman Shehu Usman