Kim Jong Un bai mutu ba
April 27, 2020Talla
Wani mashawarci ga shugaban kasar Koriya ta Kudu ne ya tabbatar da haka, yana mai watsi da jita-jitar mutuwar Kim Jong Un da ake ta yadawa.
Wata jaridar intanet ta Koriya ta Arewa ce dai ta fara fitar da labarin cewa matashin Shugaban kasa Kim Jong Un yana nan rai kwakwai-mutu-kwawai bayan da aka yi masa aiki a zuciyarsa saboda tsananin shan taba da kuma teba da yake fama da ita. Daga bisani kuma akai ta yadawa a shafukan sada zumunta cewa Kim Jong Un ya mutu a sakamakon wannan aiki da aka yi masa.
Sai dai jami'an gwamnati sun musanta wannan labari a wata hira da suka yi da gidan talabijin na CNN.