010113 Nordkorea Neujahrsbotschaft
January 1, 2013Bisa ga alamu ƙasashen Koriya ta Kudu da Koriya ta Arewa masu yaƙar juna, sun shiga shekara 2013 da ƙafar dama, sakamakon jawabin da shugaba Kim Jong UN na Koriya ta Arewa yayi, inda ya buƙaci ƙasashen biyu sun hau teburin shawara domin warware rikicin da ke tsakanin su cikin ruwan sanhi.Kasashen Koriya ta Arewa ta Koriya ta Kudu wanda ke matsayin dunƙullaliyar ƙasa sun shiga zaman doya da man ja tun bayan yaƙin da suka gwabza daga shekara 1950 zuwa 1953.Wannan yaƙi ya tabbatar da rabuwar ƙasar ta Koriya, inda Koriya ta Kudu ke samun ɗaurin gindi daga ƙasashen yammacin duniya a yayin da yakin Arewa ya samu goya bayan daga China.Tun daga wannan lokaci, hukumomin Pyong-Yang ke ci gaba da ɗaukar Koriya ta Kudu, a matsayin wani ɓangaren na ƙasarta da ya ɓalle.
A jawabin da ya gabatar albarkacin sabuwar shekara shugaban Koriya ta Arewa Kim Jong UN,ya yi fatan ganin shekara ta 2013 ta zama ta sauye-sauye da kuma gine-gine da za su taimaka domin juya babin zama saniyar ware a duniya.Sannan ya yi fatan magabatan Pyong-yang da na Seoul su ɗora tubalin da zai sake haɗe ƙasashen biyu wuri guda:
"Akwai mahimmancin kawo ƙarshen taƙƙadama tsakanin ɓangarorin biyu, wadda babu wanda ke cin moriyarta,illa asarori iri-iri da ta ke haddasa mana.Muddun mu ka ci gaba da zama cikin wannan yanayi babu maganar cigaba mai ɗorewa a gare mu."
Wannan jawabin ba zata daga shugaba Koriya ta Arewa, ya zo kwanaki kaɗan bayan da ƙasarsa ta yi saban gwajin makamai masu lizzami, wanda ya jawo sabuwar tankiya a yankin gaba ɗaya.
Tun lokacin da ake zaɓe a matsayin saban shugaban ƙasar Koriya ta Arewa a shekara 2011 masu lura da al'amurra a yankin, suka hango alamomin kawo ƙarshen rikici tsakanin Koriya ta Kudu da Koriya ta Arewa.A yanzu shugaba Kim Yong UN ya ce zai maida hankali ne ta fannin haɓɓaka tattalin arzikin ƙasa a maimakon yaƙe-yaƙe:
"Kasancewar mu ƙasa mai ƙarfin tattalin arziki a ƙarƙashin tafarkin kommunisanci ya fi fa'ida a gare mu fiye da zama kullum cikin shirin yaƙi".
Har yanzu yanzu sabuwar shugabar ƙasar Koriya ta Kudu Park Geun-hye da a ka zaɓa a watan Disemba da ya gabata, ba ta maida martani ba, game da hurucin na shugaba Kim Jong UN.
Saidai ko ba komai, wannan jawabi ƙila ya jinkirta yunƙurin Komitin Sulhu na Majalisar Dinkin Duniya wanda ke shirin ɗaukar sabin matakan ladabtarwa ga hukumomin Koriya ta Arewa.
Mawallafi: Yahouza Sadissou Madobi
Edita: Mohammed Awal Balarabe