Shugaban Koriya ta Kudu na shirye da ganawa da na Arewa
January 10, 2018Shugaba Moon Jae-In na Koriya ta Kudu ya ce yana shirye domin ganawa ta keke da keke da shugaba Kim Jong-Un na Koriya ta Arewa, wannan matsayin na zuwa yayin da kasashen duniya suka nuna maraba da amince da shirin Koriya ta Arewa na tuwa wakailai zuwa gasar Olympics na lokacin hunturu a watan gobe da Koriya ta Kudu za ta dauki nauyi, bayan tattaunawa tsakanin bangarorin biyu.
Shugaban na Koriya ta Kudu ya nuna jinjina game da tattauanwa da aka samu tsakanin bangarorin biyu. Shi dai shugaba Moon Jae-In na Koriya ta Kudu ya fadi haka yayin taron manema labari.
Tuni kwamitin kula da gasar Olympics ya yaba da matakin diplomasiya da aka cimma inda aka bayar da dama ga Koriya ta Arewa ta tura da sunan 'yan wasa daga nan zuwa lokacin da za a fara gasar, haka ya nuna sassauci da aka yi wa kasar ta Koriya ta Arewa domin tuni aka rufe rigistan 'yan wasan da za su halarci gasar, amma aka sake bude wata kafa ga kasar.