1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

An rusa gwamnatin Madagaska saboda boren al'umma

September 30, 2025

MDD ya ba da rahoton kisan mutane akalla 22 tun bayan barkewar zanga-zanga a Madagaska a ranar Alhamis da ta gabata, lamarin da ya kai shugaban kasar ga daukar matakin rusa gwamnati.

Masu zanga-zanga na fito na fito da jami'an tsaro a Madagaska
Masu zanga-zanga na fito na fito da jami'an tsaro a MadagaskaHoto: Rijasolo/AFP

A cikin wata sanarwa da ofishin kare hakkin dan Adam na MDD ya fidda, ya ce jami'an tsaron Madagaska sun kashe mutane akalla 22 da suka hada da masu zanga-zanga da wasu 'yan baruwanmu tun daga lokacin da bore ya barke a fadin kasar, inda wasu jama'a suka yi amfani da damar suka fasa shaguna domin kwasar ganima.

Tun da farko dai zanga-zanga ta barke a Madagaska a ranar Alhamis bisa kiran wata kungiya da ake wa lakabi da Gen 7 biyo bayan yawan samun katsewar wutar lantarki da ruwan sha, kanfin daga bisani ta rikide zuwa boren kin jinin gwamnati duk da matakin da shugaban kasar ya dauka na korar ministan makamashi.

Tun daga wannan lokaci matasan sun ci gaba da fantsama kan tituna a sassa daban-daban na kasar tare da yin arangama da jami'an tsaro, lamarin da ya kai shugaba Andry Rajoelina ga rusa gwamnati a ranar Litinin.

Sai dai duk da haka masu zanga-zangar da ake wa lakabi da Gen 7 sun bukaci shugaba Andry Rajoelina ya yi murabus soboda ya gaza fitar da al'umma daga kangin wahala duk da bumbin arzikin da Allah ya huwacewa tsibirin na Madagaska.