Mali: IBK ya gana da jagoran masu zanga-zanga
July 5, 2020Shugaban kasar Mali Ibrahim Boubacar Keita ya gana a wannan Lahadi da jagoran masu zanga-zangar neman sauyi a kasar wato Imam Mahmoud Dicko a gidan karbar baki na fadar shugaban kasar da ke a Bamako babban birnin kasar.
Wannan ita ce ganawa ta farko da mutanen biyu suka yi a hakumance tun bayan soma zanga-zangar wacce ta rikide zuwa tarzomar neman shugaban kasar ta Mali ya yi murabus.
Shafin Tweeter na fadar shugaban kasar ta Mali ya ruwaito jagoran masu zanga-zangar neman sauyin na cewa yana kyautata zaton idan dai da kyakkyawar aniya daga kowane bangare, za su shawo kan matsalar. Daura da wannan, Shugaba IBK ya kuma gana da wakilan jam'iyyun kawancen masu mulki.
Sau biyu dai a cikin watan Yunin da ya gabata, kawancen masu adawa da mulkin na Shugaba IBK na gudanar da kasaitacciyar zanga-zanga a birnin Bamako. Sai dai a wata sanarwa da kawancen ya fitar a ranar Larabar da ta gabata ya janye bukatarsa ta ganin Shugaba IBK ya yi murabus.