1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaGabas ta Tsakiya

Shugaban Masar ya tattauna batun tsagaita wuta azirin Gaza

Suleiman Babayo AMA
July 9, 2024

Shugaban Masar ya gana da shugaban hukumar leken asirin Amirka, CIA kan batu tsagaita wuta game da rikicin zirin Gaza tsakanin Isra'ila da mayakan Hamas.

Shugaba Abdel Fattah al-Sisi na kasar Masar
Shugaba Abdel Fattah al-Sisi na kasar MasarHoto: THIBAULT CAMUS/AFP via Getty Images

A wannan Talata Shugaba Abdel Fattah al-Sisi na kasar Masar da William Burns daraktan hukumar leken asirin Amirka ta CIA sun tattauna kan batun cimma yarjejeniyar tsagaita wuta a yankin zirin Gaza na Falasdinu mai fama da yaki, tsakanin mayakan Hamas da dakarun Isra'ila.

Wata sanarwar fadar shugaban kasar ta Masar ta jaddada matakin kasar na watsi da ci gaba da yakin da ke faruwa. Ana sa ran wakilai daga bangarorin da ke rikicin da na masu shiga tsakani za su samar da mafita kan batun na tsagaita wuta.