1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Shugaban Masar ya sauya ministan tsaron

Suleiman Babayo ATB
February 11, 2026

An nada sabon ministan tsaron a kasar Masar cikin wani sauyi da aka samu a majalisar zartaswa, inda Shugaba Abdel Fattah al-Sisi ya rantsar da sabon ministan Janar Ashraf ⁠Salem Mansour.

Shugaba Abdel Fattah al-Sisi na Masar
Shugaba Abdel Fattah al-Sisi na MasarHoto: John Macdougall/AP Photo/picture alliance

A wannan Laraba an nada Janar Ashraf ⁠Salem Mansour a matsayin sabon ministan tsaron kasar Masar. Shugaba Abdel Fattah al-Sisi ya rantsar da sabon ministan tare da wasu ministocin cikin wani takaitaccen sauyi da aka samu a majalisar zartaswar kasar. Shugaban ya yi alkawarin ci gaba da aikin bunkasa tattalin arzikin kasar.

Shi dai Janar Mansour ya maye gurbin Janar Abdel Majeed ‌Saqr, wanda yake rike da mikamun na ministan tsaron tun watan Yuli na shekara ta 2024.

Tuni dai majalisar dokokin kasar ta Masar ta amince da matakin sauyin da aka samu a ma'aikatar tsaron kasar.

 

Tsallake zuwa bangare na gaba Babban labarin DW

Babban labarin DW

Tsallake zuwa bangare na gaba Karin labarai daga DW