1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shugaban masu rinjaye a majalisar wakilan Amirka DeLay yayi murabus

January 8, 2006

Dan majalisar wakilan Amirka Tom Delay ya ba da sanarwar cewa ba zai yi kokarin sake neman mukaminsa na shugaban masu rinjaye a majalisar dokoki ba. Tom Delay dan jam´iyar Republicans na fuskantar zargi na amfani da kudi waje yin kamfen a jihar Texas, kuma yanzu haka an matsa masa lamba har yayi murabus. Delay mai shekaru 58 da haihuwa dai ya sha matsin lamba daga ´ya´yan jam´iyarsa ta Republicans game da rawar da ya taka wajen kashe kudi a hanyoyin da ba su dace ba yayin kamfen. Wani gungun ´yan majalisar sun yi kira da a sake gudanar da sabon zabe na shugaban masu rinjaye a majalisar wakilan. Da farko dai ya so ya sake tsayawa takarar neman wannan mukami bayan an kammala shari´ar a cikin watan fabrairu.