1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Shugaban mulkin sojin Burkina Faso ya kori firaministansa

Abdulkarim Muhammad Abdulkarim
December 7, 2024

Gwamnatin Laftanar Kanar Paul-Henri Sandaogo Damiba ce ta nada Mr Tambela firaminista bayan kwatar mulki daga gwamnatin dimukuradiyya ta Roch Marc Christian Kabore

Tsohon firaministan Burkina Faso da aka tsige Apollinaire Kyelem de Tambela
Hoto: Li He/picture alliance/Xinhua News Agency

Shugaban mulkin sojin Burkina Faso Kyaftin Ibrahim Traore, ya rushe majalisar shugabancin kasar da firaministanta Apollinaire Joachim Kyelem de Tambela, ba tare da bayyana dalilin rushe gwamnatin ba.

Hambararriyar gwamnatin mulkin sojin Laftanar Kanar Paul-Henri Sandaogo Damiba ce ta nada Mr Tambela firaminista, a cikin watan Oktoban shekarar 2022, bayan kwatar mulki da tsinin bindiga daga hannun gwamnatin dimukuradiyya ta Roch Marc Christian Kabore, wanda daga bisani ya samu mafakar siyasa a kasar Togo bayan kawar da shi daga karagar mulki.

Karin bayani:'Sojojin Burkina Faso na jefa rayuwar al'umma cikin hadari'

Burkina Faso na daga cikin kasashen Afirka da ke fama da juyin mulki a kai a kai, a daidai lokacin da ayyukan ta'addanci suka mamaye ta tare da kwace iko da wasu yankunan kasar.

karin bayani:'Yan ta'adda sun kashe mutane 10 a Manni na Burkina Faso

Haka zalika kasar tare da da makwabtanta Nijar da Mali sun karkatar da alakarsu ta diflomasiyya ga Rasha, bayan katse alaka da uwargijiyarsu da ta yi musu mulkin mallaka Faransa.