SiyasaAsiya
Shugaban Myanmar yana Thailand
April 4, 2025
Talla
Shugaban gwamnatin mulkin sojan kasra Myanmar, Janar Min Aung Hlaing ya isa kasar Thailand domin halartar taron kungiyar kasashen yankin, kwanaki bayan girgizar kasar da ta halaka dubban mutane a kasar ta Myanmar. Ba kasafai shugaban gwamnatin mulkin sojan yake tafiya zuwa kasashen ketere ba.
Karin Bayani: Girgizar kasa a Myanmar da Thailand
Galibin kasashen Duniya sun ba sa da wata alaka da gwamnatin mulkin sojan ta Myanmar da Janar Min Aung Hlaing yake jagoranta, tun bayan kifar da gwamnatin farar hula da Aung San Suu Kyi suke take shugabanta a shekara ta 2021.