Kasafin kudi mafi yawa a tarihin Najeriya
December 18, 2024
Najeriya dai za kuma ta biya bashin da ya kai na Triliyan 15 a shekarar dake shirin kamawar. A badin dai kuma a fada ta shugaban kasar, kasafin da ke da taken inganta tsaro da farfado da tattali na arziki dai zai kashe Naira Triliyan 4.9 wajen batun tsaron. Ilimi dai ya samu Naira Triliyan 3.5 a yayin kuma da batu na lafiya ya tashi da Naira triliyan 2.48. A badin dai kuma a fadar Shugaba Bola Ahmed Tinubu na Najeriya tana shirin kisan Naira triliyan hudu cikin ginin hanyoyi da ragowa na ayyukan raya kasa. Shugaba Tinubu dai ya ce gwamnatin kasar ta yi rawar gani wajen samun nasarar aiwatarwar kasafin kudin kasar na shekarar bana.
Karin Bayani: Kasafin kudin Najeriya ya janyo cece-kuce
Batun tsaron da kila tsada ta rayuwa dai na zaman na kann gaba a zuciyar miliyoyin al'umma ta kasar. Kasafin dai ya isa zauren majalisun kasar guda biyu daidai da wani rahoton da ke fadin 'yan kasar sun kashe Naira trilin Biyu da miliyan dubu 230 wajen biyan kudaden fansa cikin kasar a shekarar da ke shirin karewa
Majalisun kasar guda biyu dai sun amince da tsawaitar wa#adin kasafin kudin kasar na shekarar bana har ya zuwa karshen watan Yuni na shekarar mai kamawa. To sai dai kuma ra'ayi ya banbanta a tsakanin 'yan dokar bisa kasafin da ke zaman zakaran gwajin dafi ga gwamnatin da ke da burin tasiri ga rayuwa da makoma. Nasarar ta Shugaba Tinubu dai na zaman zakaran gwajin dafi ga shugaban da baya boye burin dorawa bisa mulki.