1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Tinubu: Har yanzu bai bayyana dukiyar da ya mallaka ba

December 11, 2023

Wattani shida bayan hawa bisa kujerar mulki miliyoyi a cikin Najeriya na zaman jiran sanin kaddarori na shugaba Bola Ahmed Tinubu.

Bola Ahmed Tinubu,
Bola Ahmed Tinubu, Hoto: Kola Sulaimon/AFP/Getty Images

 A kai'da ta kundin mulki dai an tsara shugaba Bola Ahmed Tinubu zai bayyana daukacin kaddarorinsa kafin hawa bisa gadon mulkin Najeriya. Ayyana dukiya ta shugabanni na kasar dai na da babban burin aiken sakon tabbatar da gaskiyya cikin harkar mulki, sannan da kwantar da hankula na 'yan kasa bisa amana ta dukiyar da 'yan mulkin ke shirin juyawa na shekaru  guda hudu.

Tinubu ya yi watanni shida kan gadon mulki bai bayyana dukiyyarsa ba

Bola Ahmed Tinubu Hoto: Temilade Adelaja/REUTERS

Tinubudai ya share watanni har guda shida ko kuma daya a cikin takwas na mulkin nasa, daga dukka na alamu ba tare da kai wa ya zuwa sanin girman kaddara da ya mallaka a halin yanzu. Ana dai kallon Tinubun, shugaba mafi kudi a tarihi na kasar, kuma dan kasuwa na farkon fari da ya dau ragamar Najeriyar a  shekaru da daman gaske. Auwal Musa Rafsanjani shugaba kungiyar Transparency reshen Nigeria mai yaki da cin hanci ya ce gaza ayyana dukiyar na zaman barazana mai girma a kokarin kasar na  yakar cin hanci.