Shugaban Najeriya ya koma gida
March 10, 2017Talla
Shugaba Muhammadu Buhari na Najeriyar ya koma gida ne da safiyar wannan Jumma'a, bayan shafe kimanin wata guda da rabi ana duba lafiyarsa a birnin London na kasar Birtaniya. Babu karin haske kan lafiyar shugaban. Ranar 19 ga watan Janairun wannan shekara da muke ciki ta 2017 ne, Shugaba Buhari ya yi balaguro zuwa Ingila domin duba lafiyar tasa. Shugaban ya sauka ne a filin jirgin saman sojoji da ke Kaduna sakamakon rufe na Abuja, saboda gyara da za a yi a kan hanyar da jiragen sama ke sauka.