Shugaban Nijar ya ce zai kare dimukuradiyya
July 28, 2023![Mohamed Bazoum](https://static.dw.com/image/66368170_800.webp)
Kwana guda bayan sanar da kwace gwamnati, hambarerren Shugaba Mohamed Bazoum na Jamhuriyar Nijar ya sha alwashin kare nasarorin dimukuradiyyar da ya ce an same su da tsayin daka.
A daren ranar Larabar da ta gabata ce dai sojoji a Nijar din suka ayyana kwace iko daga Bazoum, suka kuma rusa kundin mulki tare da dakatar da duk wani tsari na farar hula a kasar.
Mohamed Bazoum wanda ba a kaiga sanin inda yake ba tun bayan aukuwar lamarin, ya yi alkawarin cewa 'yan Nijar masoya dimukuradiyya ne ke da nasara a karshen wannan lamari.
Kasar Amurka da ma Majalisar Dinkin Duniya, duk sun yi alkawarin bai wa Bazoum cikakken goyon baya a halin da yake ciki.
Wannan ne juyin mulki karo na bakwai da ake gani a yankin yammaci da ma tsakiyar Afirka, daga shekara ta 2020 zuwa yanzu.