1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shugaban Nijar ya nemi tallafi daga Faransa

Abdoulaye mamane AmadouJune 15, 2016

Wani sabon cece-kuce ya kunno kai a Jamhuriyar Nijar bayan da Shugaba Issoufou Mahamadou ya nemi tallafin sojojin kasar Faransa kan yaki da Boko Haram.

Frankreich Niger Präsident Mahamadou Issoufou in Paris bei Francois Hollande
Shugaba Mahamadou Issoufou na Nijar, da Fransoi Hollande na FaransaHoto: M. Alexandre/AFP/Getty Images

Ziyarar ta shugaban kasa Issoufou Mahamadu a Paris na zuwa ne makonni biyu kawai bayan mayakan Boko Haram sun kai wani mumunar farmaki a garin Bosso da ke jihar Diffa, inda suka halaka sojojin kasar ta Nijar da na Najeriya 26. Wannan harin ya yi sanadiyar kauracewar jama'a kusan dubu 50 daga garuruwa don samun mafaka a wasu garuruwan na daban.

Wannan dai ita ce ziyara ta biyu da shugaban kasar yake kaiwa a wata kasa da zummar neman dauki don magance matsalolin ta'addanci cikinsu har da matsalar ta Boko Haram da ke neman ta gagari kundila a jihar ta Diffa, inda ziyarar ta farko ya kai ta a kasar Chadi.

Sai dai jama'a na ci-gaba da tofa albarkacin baki kan matakin na kokon bara da shugaban kasar ta Nijar ya dauka a yakin da suke da 'yan ta'dda, musamman ma mayakan Boko Haram. Farfesa Issoufou Yahaya wani mai sharhi ne a harkokin tsaro kuma malami a jami'ar birnin Yamai:

Shugabannin Nijar, Najeriya da ChadiHoto: State House, Abuja


"Ba za ka ce wani zai maka tsaro ba, kai kana nan sai wani ya gani ya gaya maka a'a kuma 'yan Boko Haram din nan ma harshe daya muke da su, kenan wanda yake Diffa shi ne ka iya bayyana wa gwamnati labari kai har ma ya bai wa nasaru labari tatacce ba wai ya jira nasaru su bashi labari ba."

Jamhuriyar Nijar dai na fuskantar barazanar ta'addanci a wasu iyakokinta da kasashe kamar Mali da Libiya, inda 'yan ta'dda suke da gindin zama da kuma uwa uba Najeriya inda Boko Haram ke cin karenta babu babbaka. Sai dai ga wani dan rajin kare hakin dan adam Malam Sidi Fodi Hamidou maganar neman tallafin kasashe kamar su Faransa ba zai yi wani tasiri ba:


" Ai can wajen Diffa akwai sojojin na Faransa lokacin da aka kai farmaki a kwanaki, na yi imani da Allah inda da gaske mutanen nan suke cewa za su taimakonmu, da ba za su bari akai muna farmaki ba. Mu abin da muke so shi ne Mahamadou Issoufou ya gane cewa idan an bai wa sojojin Nijar kayan aiki, ba shakka wannan abin ba zai faru domin sojan Nijar baya gudu ."

Wani sojan kasar Faransa a MaliHoto: picture-alliance/AP Photo


Ba tun yau ba dai hukumomin kasar ta Nijar ke ambato daukar matakai don dakile matsalolin na ayyukan ta'addanci dalillan da suka kai ga Daouda Tankama na kungiyar Muryar talaka cewar su kam su na goyon bayan duk wani tallafin da zai iya taimaka wa kasar ta Nijar ta sake dawowa da martabarta a idon jama'a ganin irin halin tagayyarar da ayyukan ta'adanci ke yi a yanzu.

Tun da jimawa ne dai kasar Faransa take da hulda ta kut da kut da Jamhuriyar Nijar musamman ma fannin yaki da ta'adanci, inda ta girke sansani sojojinta da dama a kasar wadanda sojojinta na Barkhan ke amfani da su.