SiyasaGabas ta Tsakiya
Shugaban Pakistan ya rusa majalisar dokoki
April 3, 2022Talla
Shugaban kasar Paksitan Dr. Arif Alvi, ya rusa majalisar dokokin kasar a wannan Lahadi. Matakin ya biyo bayan yunkurin tsige Firaminisatan kasar Imran Khan ta hanyar kada masa kuri'ar yankan kauna da 'yan majalisar kasar suka yi. Mataimakin shugaban majalisar ta Pakistan ne dai ya dakatar da yunkurin, in da ya ce kudurin ya saba wa dokokin kasar.
Pakistan dai tana da tarihin rikicin shugabanci kala-kala. Tun daga shekara 1947, lokacin da kasar ta samu 'yancin kai daga Turawan Birtaniya, babu firaministan da ya taba yin cikakken wa'adin shekaru biyar ba tare da an yi masa juyin mulki ko kuma rikicin siyasa ya kawar da shi ba. A shekara ta 2018 ne dai Firaminista Khan mai ci ya hau mukamin.