Shugaban Pakistan ya tube kakinsa na Soja
November 28, 2007Talla
Shugaban mulkin soja na Pakistan Parvez musharraf ya sauka daga matsayinsa babban hafsan sojojin ƙasar wajen wani biki da akayi a birnin Rawalpindi.Gidan TV na kasar ya yayata bikin kai tsaye inda Musharraf ya miƙawa kansa mulki daga soja zuwa farar hula.Musharraf wanda ya ƙwaci mulki a 1999 ya miƙa jagorancin rundunar sojin hannun Janar Ashfaq Kiyani wanda ya gaje shi.A ranar Alhamis zaa rantsar da Musharraf a matsayin shugaban farar hula.Har yanzu dai Pakistan tana cikin dokar ta ɓaci wadda Musharraf ya kafa a ranar 3 ga watan Nuwamba yana mai baiyana cewa ana bukatar dokar don kare rikicin sojojin sa kai na islama.