Shugaban Rasha Vladimir Putin ya yi tazarce
March 17, 2024Sakamakon farko na kuri'un da aka kirga na nuni da cewa Shugaba Putin ya lashe zaben shugaban kasar da aka gudanar da kaso fiye da 87 cikin 100 kamar yadda hukumar zaben kasar ta nuna.
Fadar White House ta Amurka ta soki yadda sakamakon zaben tare da bayyana cewa an gudanar da zaben ne ba tare da 'yan hamayya ba ganin cewar daukacin masu adawa da Shugaba Putin na tsare a gidan yari.
A ranar Lahadi aka kammala kada kuri'a a zaben shugaban kasar Rasha, wanda tun daga farko aka ayyana Shugaba Putin da ke cikin 'yan takara a matsayin wanda ka iya lashe zaben.
Mai shekaru 71 a duniya, sakamakon zaben zai ba wa Shugaba Putin damar zarcewa kan madafan iko a wani sabon wa'adi na shekaru shida kan madfafan iko bayan ya kwashe shekaru 20 yana kan karagar mulki.