1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaJamus

Shugaban Senegal zai sasanta ECOWAS da AES

Binta Aliyu Zurmi
July 8, 2024

Kungiyar raya tattalin arzikin yammacin Afirka ECOWAS ta nada Shugaban kasar Senegal Basirou Diomaye Faye a matsayin wanda zai shiga tsakaninta da shugabannin kasashen Nijar da Mali da Burkina Faso.

Ecowas-Treffen in Nigeria | Bola Tinubu
Hoto: Gbemiga Olamikan/AP/dpa/picture alliance

Kungiyar ta ECOWAS ta nemi Shugaba Faye na Senegal da ya shawo kan shugabanni uku da suka yi musu tawaye bayan karbe madafun iko da tsinin bindiga a kasashensu, daga baya kuma suka kafa tasu kungiyar wanda ECOWAS ta ce rarabuwar kawuna da ke tsakanin kasashen yammacin Afirka na zama barazana ga tsaronsu.

A ranar Asabar din da ta gabata ce, shugabannin kasashen Nijar da Mali da Burkina Faso suka gudanar da babban taronsu a karon farko karkashin kungiyar AES a birnin Yamai na Jamhuriyar Nijar, tare da tabbatar da raba gari da kungiyar ECOWAS.

Shugabannin kasashen ECOWAS a taronsu da ya gudana a ranar Lahadi a birnin Abuja na Najeriya sun sake zaben Shugaba Bola Tinubu a matsayin shugabann kungiyar.

Wannan shi ne karon farko a kusan shekaru 50 da kungiyar ta ECOWAS ke rasa mambobinta a irin wannan siga.

 

Karin Bayani : ECOWAS ta ja hankalin kasashen AES kan ficewa daga kungiyar