1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shugaban Sin Hu Jintao ya fara ziyara a Nigeria

April 26, 2006

Da yammacin yau ne shugaba Hu Jintao na kasar Sin ya sauka a tarayyar Nigeria dake zama kasa mafi girma dake da arzikin man Petur a Afrika.Manazarta sun bayyana ziyarar ta shugaba Hu a kasashen Afrika guda 4 da yankin gabas ta tsakiya,da kasancewa damar inganta huldar dangantaka ta cinikin mai da kasashen ,adaidai lokacin da bukatun Sin da harkokin makamashi da mai na duniya ke dada tashin gwauron zabi.

Shugaba Olusegun Obasanjo na tarayyar ta Nigeria ne ya taryi takwaransa na Sin a Abuja,a farkon wannan ziyara tasa ta yini 2,.Ana saran shugabannin biyu zasu tattauna,kana shugaba Hu zaiyi jawabi way an majalisar dokokin kasar guda biyu.A wata sanarwar da aka gabatarwa manema labaru,shugaba Hu yace ,ziyarar tasa zata taimaka wajen inganta dangantaka tsakanin Nigeria da Sin a fannoni daban daban,inda zasuyi aiki kafada da kafada.

Gwamnatin Sin dai zata zuba jarin dala billion 4 wajen sake farfado da kanfanin tache danyan mai dake kaduna,inda amadadin haka Nigeria zata bata lasisin hakar mai na kamfanoni hudu.