1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shugaban Sudan zai ziyarci Sudan ta Kudu

April 12, 2013

Umar Hassan El Bashir zai tattauna batun tsaro da na albarkatun man fetir tsakanin sa da takwaransa na Sudan ta Kudu Salva Kiir

[28898211] Sudan's President Omar Hassan al-Bashir visits Libya epa03052531 Sudan's President Omar Hassan al-Bashir talks to media at a joint press conference with Libya's National Transitional Council (NTC) chairman Mustafa Abdul Jalil (unseen) following their meeting in Tripoli, Libya, 07 January 2012. Sudanese President Omar al-Bashir used a visit to Libya to accuse the slain leader Muammar Gaddafi of causing suffering to both the Libyans and Sudan. Al-Bashir and Gaddafi had an uneasy relationship, as Khartoum had accused Gaddafi of helping Darfur rebels against Sudanese government forces. EPA/SABRI ELMHEDWI +++(c) dpa - Bildfunk+++
Hoto: picture-alliance/dpa

Ziyarar wace ita ce ta farko da shugaban na Sudan zai kai a yar ƙaramar ƙasar da ta sami yanci gashin kai, bayan wata ƙuria ta raba gardama da aka yi a cikin watan Yuli na shekara ta 20011.Na zaman wata kafa ta ƙara ƙarfafa hulɗa da dangantaka tsakanin ƙasashen biyu, bayan da aka kwashe lokaci mai tsawo suna kabsa yaƙin basasa kafin ɓalewar Sudan ɗin ta Kudu.

An shirya shugabannin biyu zasu tattauna batun tsaro da na yanki Abyei mai arzikin man fetir wanda ƙasashen biyu ke iƙirarin mallaka. A makon jiya ne dai hukumomin Sudan ta Kudu suka sanar da sake tura man fetir ɗin da suke haƙowa zuwa Sudan. Tun da farko an dakatar da shirin ne kusan shekara guda akan zargin da Sudan ta Kudu ɗin ta yi cewar Sudan na tswala kuɗaɗen fito tare kuma da satar man na su.

Mawallafi : Abdourahamane Hassane
Edita : Usman Shehu Usman