Shugaban Tarayyar Afirka ya isa Burkina Faso
November 10, 2014Talla
Da yake magana a gaban manema labarai Shugaba Ould Abdel Aziz ya ce Tarayyar Afirka ba tazo don yin hukunci ba, amma tazo ne domin tallafawa bengarorin wannan kasa a kokarin da su ke na samun mafita. Da safkar sa a filin jirgin saman birnin Ouagadougou, shugaban na Tarayyar Afirka ya samu tarbo daga Kanar Yacouba Isaac Zida da a halin yanzu yake jagorantar kasar ta Burkina Faso kafin a samu wanda zai jagoranci gwamnatin rikon kwaryar kasar daga bangaren farar hula. A ranar uku ga watan Nowamba ce dai Tarayyar Afirka ta bai wa sojojin kasar wa'adin mako biyu na mayar da mulki ga hannun fararen hula.
Mawallafi: Salissou Boukari
Edita : Suleiman Babayo