Shugaban Tunisiya ya kama hanyar lashe zabe
October 7, 2024Shugaba Kais Saied na Tunisiya ya kama hanyar lashe wa'adi na biyu na mulkin kasarsa, bayan da kididdigar jin ra'ayin jama'a da aka gudanar bayan zaben ranar Lahadi ta nunar da cewa ya samu kashi 89.2% na kuri'un da aka kada. Dama an yi hasashen cewar zai samu gagarumin rinjaye saboda ana zargin Saied da amfani da salon mulkin kama karya wajen kawar da abokansa na hamayya.
Karin bayani: Fushin matasa na kara tsananta gabanin zabe a Tunisiya
Hukumar zaben Tunisiya ta nunar da cewar kashe 27.7% na wadanda suka yi rejista ne suka kada kuri'a, adadin da ke zama mafi karanci tun bayan gika tsarin demukuradiyya a Tunisiya a shekara 2011 bayan hambarar da mulkin kama-karya na Ben Ali. 'Yan adawa biyu da ba su da karfin fada a ji ne aka ba su damar tsayawa takara daga cikin mutane 17 da suka mika takardun zawarcin kujerar mulkin kasar. Kungiyoyi masu zaman kansu na ciki da wajen Tunisiya sun yi tir da kamun ludayin hukumar zaben kasar wacce suka danganta da 'yar amshin shatar Kais Saied.