Shugaban Turkiya ya caccaki 'yan awaren Kurdawa
July 28, 2015Talla
Shugaba Racep Tayyip Erdogan na kasar Turkiya ya ce babu yadda za a ci gaba da tattaunawa da 'yan awaren Kurdawa sannan ya nemi majalisar dokokin kasar ta cire kariya wa 'yan majalisa da suke da nasaba 'yan awaren domin fuskantar tuhuma.
Shugaban ya fadi haka jim kadan bayan dakarun sama na kasar sun kai farmaki kan sansanonin 'yan awaren da ke arewacin kasar Iraki, sakamakon hari kan sojojin kasar. A wannan Talata yayin taron gaggawa na kungiyar tsaro ta NATO a birnin Brussels na kasar Belgium, Turkiya ta samu goyon baya na siyasa kan hare-hare a kan tsagerun kungiyar IS a cikin Siriya, da kuma 'yan waren Kurdawa.