Erdogan ya zargi Tarayyar Turai da taimakon ta'addanci
November 6, 2016Talla
Shugaban kasar Turkiya Recep Tayyip Erdogan ya zargi tarayyar Turai da taimakawa ta'addanci ta hanyar goyon bayan kungiyar Kurdawa ta PKK. Ya ce bai damu da abin da Tarayyar Turai za ta fada a kansa ba ko za ta kira shi mai mulkin kama karya ne, yayin da yake ci gaba da yin dirar mikiya a kan Kurdawa 'yan fafutuka da masu goya musu baya.
Kasar Turkiyar dai ta fuskanci kakkausar suka daga kasashen duniya sakamakon kama shugabanin jam'iyyar adawa ta Kurdawa HDP tare da wasu 'yan majalisar dokokin Jam'iyyar. Gwamnatin ta na zargin jam'iyyar ta HDP da alaka da kungiyar PKK, zargin kuma da jam'iyyar ta musanta.