1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaTurai

Shugaban Ukraine ya ce Rasha ta fara yakin duniya na uku

Abdulkarim Muhammad Abdulkarim
February 23, 2026

Shugaba Volodymyr Zelensky na Ukraine ya ce abin da ya rage shi ne jiran ganin adadin kasashen da Rasha za ta mamaye.

Yadda makaman Rasha suka ragargaza gine-gine a birnin Kyiv na Ukraine ranar 22.02.2026Kyjiw 2026
Yadda makaman Rasha suka ragargaza gine-gine a birnin Kyiv na Ukraine ranar 22.02.2026Kyjiw 2026Hoto: Valentyn Ogirenko/REUTERS

Shugaba Volodymyr Zelensky na Ukraine ya ce a fahimtarsa tuni takwaransa na Rasha Vladimir Putin ya kunna wutar fara yakin duniya na uku, abin da ya rage shi ne jiran ganin iya adadin kasashen da zai mamaye.

Mr Zelensky na wannan ikirari a tattaunawarsa da BBC ranar Lahadi, gabanin cika shekaru hudu da barkewar yakin, wanda aka fara a ranar 24 ga Fabarairaun 2022.

Karin bayani - Afirka ta Kudu ta nemi dawo da mutanenta da ke yakin Rasha

Ya kara da cewa kasarsa wadda ta yi dogaro da Amurka, don ba ta kariyar tsaro, tana zuba idon ganin ingantaccen agajin da za ta samu daga gare ta.