Shugaba Zelenskiy zai tattauana da G7
December 12, 2022Shugabannin gaggan kasashe bakwai masu karfin masana'antu na G7, za su tattauna da shugaban Ukraine Volodymyr Zelenskiy ta hanyar bidiyo, kamar yadda mai magana da yawun gwamnatin Jamus ya sanar.
Shugaban gwamnatin Jamus Olaf Scholz, shi ne zai jagoranci taron wanda ke zuwa kafin karshen wa'adin Jamus din a shugabancin kungiyar ta G7.
Yayin wani taron manema labaru a birnin Berlin, hukumomi sun ce babu batun samar da makamai ga Ukraine daga cikin abubuwan da za a tattanuna a taron na yau.
Sai dai kuma tattaunawar, ta zo ne kwana guda bayan wata da Shugaba Zelenskiy ya yi da Shugaba Joe Biden na Amirka, inda Amirkar ta da tabbacin ci gaba da taimaka wa Ukraine, musamman ganin yadda Rasha ke tsananta hare-hare kan tashoshin samar da wutar lantarkinta.
Galibin yankunan Odessa da ke kudancin Ukraine dai a yanzu na rayuwa ne babu wutar lantarki.