1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Shugaban Yuganda ya ce masu shirin bore su guji wasa da wuta

Abdulkarim Muhammad Abdulkarim
July 21, 2024

Yoweri Museveni ya yi zargin cewa ingiza su ake yi daga ketare, a don haka ba zai saurara wa matasan ba

Hoto: Darko Vojinovic/AP Photo/picture alliance

Shugaban kasar , ya gargadi matasan da suka shirya gudanar da zanga-zangar nuna fushi da tsanantar cin hanci da rashawa a kasar ranar Talata, da su sani cewa tamkar suna wasa da wuta, tun da gwamnati ta riga ta haramta musu fita.

Karin bayani:Uganda Yoweri Museveni

Jan kunnen na Mr Museveni na zuwa ne lokacin da yake jawabi ta gidan talabijin din kasar ranar Asabar, yana mai cewar suna da masaniyar cewa ingiza su ake yi daga ketare, a don haka ba zai saurara wa matasan ba matukar suka fito don yin boren.

karin bayani:Rikicin kasuwanci tsakanin Amurka da Yuganda

Tuni dai rundunar 'yan sandan yuganda ta sanar da shirinta na dakile duk wani yunkuri na tayar da tarzoma a Kampala babban birnin kasar ranar Talata mai zuwa, kasancewar akwai bayanan sirrin da suka samu da ke nuna cewa wasu bata-gari sun kuduri aniyar fakewa da ita don tayar da husuma a kasar.

Kenya da ke makwabtaka da Yganda, ta fuskanci jerin zanga-zangar nuna adawa da gwamnati, tare da kiran shugaba William Ruto da ya sauka, lamarin da ya janyo mutuwar mutane sama da 50.