Shugaban Zambiya ya suma a lokacin biki
March 8, 2015Shugaban ƙasar Zambiya Edgar Lungu ya yanke jiki ya faɗi a lokacin da ya ke halartar bikin ranar kare 'yanci mata da ya gudana a Lusaka babban birnin kasar. An dai garzaya da shi asibitin soji cikin gaggawa domin bashi kulawa da ta dace. sai dai kuma cikin wata sanarwa da ta fitar, fadar shugaban kasa ta yi kira ga al'umma da suka kwatar da hankulansu, saboda gajiya ce kawai ke damun shugaban da kuma zazzabin cizon sauro.
Sai dai kuma 'yan adawa na zargin shugaba Lungu da marar ciwon sukari watau Diabetis. Shugaban na Zambiya mai shekaru 58 a duniya ya dare kan juerar mulki ne watannin biyun da suka gabata bayan rasuwar Micheal Sata a lokacin da ya ke tsaka da wa'adinsa na mulki. Marigya Michael sata ya zama shugaba na biyu da ya mutu a cikin shekaru shida a kan karagar mulki. 'yan siyasar kasar da dama sun ta nema a fara duba lafiyar kowani dan takara kafin a bashi damar shiga a dama d shi a zabe, amma kuma hakarsu ta kasa cimma ruwa.