Shugaba Kagame zai sauka daga mukamin shugabancin AU
February 10, 2019Talla
Jagorancin kungiyar na zagayawa ne tsakanin yankuna biyar na nahiyar Afirka, batun yawaitar rikice-rikice ne kan gaba cikin batutuwan da shugabannin kasashe 55 na kungiyar za su tattauna, da yake jawabi kafin taron babban magatakardan Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres ya baiyana zabubbukan da suka gudana a Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwango da Mali da kuma Madagaska a matsayin abin a yaba, ya kuma kara da cewar a yanzu Afirka ta fara zama abin misali ga sauran kasashe sakamakon irin yadda aka samu ingantuwar alaka tsakanin kasashen Habasha da Eritiriya da Sudan ta Kudu da kuma Afirka ta tsakiya.