Shugabanin G20 za su tsaurara tsaro
November 15, 2015Shugabannin kasashen duniya da ke halarto taron G20 a birnin Antalya na kasar Turkiyya sun ce za su matsa kaimi wajen sanya idanu kan iyakokinkin kasashensu biyo bayan harin birnin Paris na Faransa.
Kasashen wadanda ke kan gaba wajen karfin tatalin arziki suka ce za su kasance tsintsiya madaurinki daya wajen yakar dukannin wani nau'i na ta'addanci a kasashen duniya kana za su yi bakin kokarinsu wajen ganin an magance kwararar bakin haure da 'yan gudun hijira.
A taron nasu da suka fara dazu dai sun yi Allah wadai da irin yadda aka hallaka mutanen da ba su ji ba su kuma gani ba, a sassan Paris daban-daban inda suka ce harin gare su baki daya ba wani Faransa ita kadai ba.
Nan gaba a yau ne ake sa ran za a fidda wata sanarwa a hukumance kan cikakken matsayin shugabannin kasashen da ke halartar taron na G20.