1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shugabanni a Kataloniya za su kai kara MDD

Yusuf Bala Nayaya
February 1, 2018

A cewar lauyansu Ben Emmerson tsarewar da mahukuntan kasar Spain suka yi masu an tsarata ne don hana masu dama ta shiga harkokin siyasa.

Spanien Sitzung des katalanischen Parlaments in Barcelona
Zaman majalisa a yankin KataloniyaHoto: Reuters/A. Gea

Shugabanni uku daga yankin Kataloniya da aka dauresu a Spain sakamakon shigarsu dambaruwar siyasar yankin a kokarin ballewa daga kasar Spain sun bayyana cewa za su kai kukansu ga 'yan fafutika na Majalisar Dinkin Duniya kamar yadda lauyansu a birnin London ya bayyana a wannan rana ta Alhamis.

A cewar lauyansu Ben Emmerson tsarewar da mahukuntan kasar Spain suka yi masu an tsarata ne don hana masu dama ta shiga harkokin siyasa a matsayinsu na wakilan al'ummar yankin Kataloniya. Lauya Emmerson ya bayyana haka ne a wani taron manema labarai da ya kira a wannan rana.