Shugabanni EU na neman mafita ga rikicin Siriya
December 15, 2016Galibin shugabannin kasashen Turai wadanda suka hallara a birnin na Brussels sun nuna takaicin rashin iya samun mafita kan rikicin na Siriya, duk da yadda aka dauki lokaci na neman hanyoyin warware abin da ke faruwa. Sai dai a cewar Firamnista Stefan Lofven na kasar Sweden ya dace a duba wannan lamari na Siriya da ido basira:
Ya ce "Ban ji dadi ba. Ina tutanin haka kowani minti guda. Na gana da masu kula da harkokin jinkai na Tarayyar Turai domin sanin abin da ya fi dacewa domin a yi na taimakon farko. Mutane ya dace su iya barin yankin, ana kai hari kan fararen hula. Har motocin daukan marasa lafiya ana kai musu hari. An wuce makadi ra rawa tun tuni. Babu wanda zai yarda da haka. Agaji a farko. Daga nan sai mu yi magana saboda ya dace a dauki mataki anan nake gani."
Batun Brexit ya auki hankalin taron EU
Kungiyar Tarayyar Turai tana ganin tabbatar da kare fararen hula a halin da ake ciki shi ya fi muhimmanci. Ci gaba da samun kwararan bakin haure zuwa kasashen Turai na cikin abubuwa da suke sukurkuta lamura ga 'yan siyasa, kuma ake neman mafita. Firamnista Therersa May ta Birtaniya ta ce ya dace a dauki matakin bai daya. Kana May ta ce ana bukatar samun hanyoyin da suka dace domin tabbatar da fitar Birtaniya daga cikin Tarayyar Turai ba tare da samun wata matsala ga bangarorin biyu.
Sannan ta kara da cewa:"A karshe ina maraba da sauran shugabanni domin tattauna yadda Birtaniya za ta fice daga kungiyar Tarayyar Turai yayin da muke shirin fara amfani da yarjejeniyar kungiyar mai lamba 50 zuwa karshen watan Maris na shekara mai zuwa, ya dace sauran shugabannin su shirya kamar yadda muke shiryawa."
Firamnista Theresa May ta Birtaniya ta kara da cewa suna bukatar ganin an samu hanyar kare bukatun bangarorin yayin da kasar ta fice daga cikin kungiyar. Ana sa bangaren Shugaba Francois Hollande na Faransa ya nemi karin agaji ga kasar Girka wadda ta fuskanci rudani na rashin kudi.
Ya ce "Na yarda da matsayin Eurogroup, wadda ta amince da shirin saukaka bashin da ake bin kasar Girka. Duk da yake ana bukatar kara samun matakan da za su mutunta da samar da mafita kan kasar ta Girka."
Wasu batutuwa da ake tattaunawa yayin taron da kungiyar Tarayyar Turai sun hada da tsawaita wa'adin takunkumin da Tarayyar Turai ta saka wa Rasha dangane da batun mamayar gabashin Ukraine da batun shirin kama aikin sabuwar gwamnatin Shugaba Donald Trump a Amirka.