Bukatar tashi tsaye domin kare muhalli
September 23, 2019Thunberg ta bayyana hakan ne yayin taron da sakatare janar na Majalisar Dinkin Duniyar Antonio Guterres ya kira, kan sauyin yanayi a birnin Newe York na Amirka, inda ta ce shugabannin sun kwaye musu baya ta hanyar gaza magance matsalar fitar hayakin masana'antu da ke gurbata muhalli. Greta Thunberg dai ta gana da shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel. Guterres ya kira wannan taron ne da nufin zaburar da shugabannin kasashe kan bukatar tabbatar da aiwatar da yarjejeniyar kare muhallin da aka cimma a birnin Paris na kasar Faransa, yarjejeniyar da kasashe 66 suka amince da ita ta hanyar shan alwashin dakile gurbatar muhallin nan da shekara ta 2050. Sai dai shugaban kasar Brazil Jair Bolsonaro da a yanzu haka ksarsa ke fuskantar babbakewar dajin Amazon da ke da matukar muhimmanci ga iskar da duniya ke samu, bai halarci wannan taron ba. A jawabinsa shugaban Kiristoci mabiya darikar Katolika na duniya Fafaroma Francis ya bukaci shugabannin al'umma da su tabbatar sun dauki matakan yaki da sauyin yanayin da gaskiya, kasancewar sauyin yanayin na zaman babbar barazana da duniya ke fuskanta.