Shugabanni sun shirya wa murkushe Boko Haram
November 29, 2022Sama da dalar Amirka miliyan 200 ne dai aka kai ga batarwa, ko bayan dubban sojoji a cikin yankin tafkin Chadi, duk dai a cikin neman kai karshen matsalar Boko Haram. To sai dai kuma shugabannin kasashen yankin sun ce sun fara ganin haske a kokari na kai karshen annobar zuwa gidan tarihi. Wajen wani taro na kasashen yankin guda shida a Abuja dai, shugabannin da suke fadin sun sha karfin kungiyar dai sun ce ana bukatar turin karshe da nufin kare ayyuka na Boko Haram a daukaci na tafkin Chadi.
Shugaba Buhari da ke jagorantar kungiyar kasashen yankin dai ya ce a shirye masu siyasar suke da su ba da daukaci na bukata da nufin sare kan macijin da ke ta shure-shure. Duk da cewar dai akwai alamun juyuwar reshe a cikin yakin da ke kallon karuwar cin dunun masu ta'addar, daga dukkan alamu akwai jan aiki a tsakanin jami'an tsaron da kaiwa ya zuwa kare ayyuka na kungiyar da ke tashi da lafawa yanzu.
Ko a cikin makon da ya shude alal ga misali, ‘ya'yan kungiyar ISWAP sun yi nasarar hallaka sojojin Chadi kusan 40. To sai dai kuma a fadar Ambasada Mamman Nuhu da ke zaman shugaban hukumar gudanarwar tafkin Chadin, ana samun gagarumin ci gaba a kokari na kare ayyuka na kungiyar ta Boko Haram.
Karancina kudi game da matsalar isassun kayan aiki da ma bambanci na tunani a bangaren sojoji na kasashen yankin dai, na zaman babbar matsala da ke tarnaki ga samun nasarar sake tabbatar da zaman lafiya a cikin kasashen. Kafin sabon umurnin da a cewar Manjo Janar Abdul Khalifa Ibrahim da ke jagorantar sojoji na hadin gwiwar tafkin Chadin ke shirin sauya da dama a cikin yakin.
Sama da mutane miliyan 30 ne dai ke rayuwa a tafkin Chadin da ke zaman daya a cikin mafi girma a nahiyar Afirka kafin janyewa da kafewar da ta haifar da sauyin yanayi da ma rigingimu na rayuwa a cikinsa.