Shugabannin APC sun dira a jihar Rivers
November 6, 2013Babbar jam'iyyar adawa ta APC a Najeriya ta gayyaci bangaren sabuwar jam'iyyar PDP a Jihar Rivers, don hadewa a yi tafiya daya domin kafa sabuwar gwamnati a Najeriya. Sai dai daga furuce-furuce da aka yi a gurin wannan taro, da alama adawar siyasa a Najeriya tana kara zafafa.
Bayan bude taro da kade-kade da raye-raye, da suka gudana a cikin harabar gidan gwamnatin Jihar ta Rivers, inda dubban magoya baya suka halarta. Akwai jawabai da gaggan 'yan jam'iyyar ta APC suka gabatar. Daga masu jawaban akwai Bola Ahmad Tinubu da ya bayyana takaicin dalilan da ya sa taron bai gudana a wannan Litinin (04. 11. 13) ba, kamar yadda aka tsara, sai wannan Talatar (05. 11. 13) .
Ya ce "Ba ma son tashin hankali ko yamutsi, so muke mu zo jihar Rivers cikin kwanciyar hankali, don mu sadu da kowa a nan, bisa neman hadin kanku a tafiyar siyasa tare. Shi ya sa muka ce a samu nutsuwa, muka daga taron sai yau Talata"
Taron dai, na neman hadin kan jihohin da gwamnonin PDP bakwai da ke yi wa uwar jam'iyyarsu tawaye, don su shiga jam'iyyar APC a yi tafiya tare a siyasar 2015.
Bayan dai gabatar da jawabi cikin Turanci da shugaban tawagar ta jam'iyyar APC, wato Janar Muhammadu Buhari ya yi, inda ya nemi jama'ar jihar Rivers su shigo a yi tafiya tare, Janar din ya kara wa wakilinmu Muhammad Bello bayani, kan zabubbukan kasar
Buhari ya ce "babban abin shi ne a tabbatar an yi zabe kan ka'ida don duk abin da muke yi ba za a bari ayi zaben ba, zuwa za ai a rubuta, aje gidan rediyo a fadi, ace in mutum yana da magana ya tafi wurin shari'a, to abin ba zai yi wu ba. Saboda haka wannan ya danganta ga 'yan Najeriya, dukkansu su tabbatar sun zabi wadanda suke so su wakilce su, su kuma shugabance su"
Da yake mayar da jawabi a maimakon jama'ar jihar Rivers, Gwamna Rotimi Amaechi, ya fara da yin jawabin na hannunka mai sanda , inda yace.
"Kamata ya yi mutum ya san cewar in har ka yarda da Ubangiji, to babu kuma shayin wani. Kuma an sha za a cire ni daga gwamna, tun shekara ta 2007, amma har yau ina nan daram"
Daga karshe dai Gwamna Amaechi ya nunar cewar ya ji gayyatar ta jam'iyyar APC, kuma za a yi shawara da jama'ar Rivers da kuma gwamnoni bakwai na kasar, kafin yanke hukunci.
Wannan taro dai da aka yi kusan kukan kurciya ne, tare kuma da fitowa karara don yin adawa da fadar gwamnatin Najeriya, a daya daga zuciyar jihohin yankin Niger Delta, inda shugaba Goodluck Jonathan ya fito. Masu sharhin siyasa na hangen cewar, labudda akwai kallo ga mai yawan rai a siyasar 2015, bisa la'akari da yadda adawa ke dada ruruwa daga yankin da shugaban kasar ya fito.
Mawallafi: Muhammad Bello
Edita: Usman Shehu Usman