1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaArewacin Amurka

Shugabannin BRICS sun bukaci kawo karshen yakin Gaza

July 6, 2025

Shugaba Luiz Inacio Lula da Silva ya ce bai kamata su zuba ido ba kan yadda Isra'ila ke kashe fararen hula da kuma amfani da 'yunwa a matsayin makamin yaki ga al'ummar Gaza ba.

Shugabannin kungiyar BRICS a birnin Rio de Janeiro na Brazil
Shugabannin kungiyar BRICS a birnin Rio de Janeiro na BrazilHoto: Pilar Olivares/REUTERS

Shugaban kasar Brazil Luiz Inacio Lula da Silva ya jaddada kira ga kasashen duniya wajen kawo karshen abin da ya kira karshen "kare dangi" da Isra'ila ke yi a Gaza, a daidai lokacin da shugabannin kasashe 11 masu karfin tattalin arziki na BRICS ke kammala taronsu a birnin Rio de Janeiro.

Karin bayani: BRICS na tsara tunkarar manufofin shugaban Amurka Trump 

An dai samu rarrabuwar kawuna dangane da yadda kasashen na BRICS ke nazari kan yakin Gaza da kuma bayyana ra'ayinsu kan gumurzun kwanaki 12 da Isra'ila ta yi da Iran. Kalaman Shugaban Brazil na zuwa a daidai lokacin ake sa ran Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu zai gana da Donald Trump a gobe Litinin 8 ga watan Yuli, a can fadar White House na Amurka.