Shugabannin China masu ci da gumin talakawa
November 8, 2012Ya zuwa yanzu dai babu wani abin da aka sani tabbatacce game da yadda manyan shugabannin siyasa na China suke tafiyar da harkokinsu na kasuwanci. To sai dai ana sane da cewar shugabannin jam'iyar kwaminis da na gwamnatin kasar cikin dare daya sukan zama masu arzikin gaske. Jaridar New York Times ta rawaito cewar iyalan Pirimiya Wen Jiabao sun tara dukiyar da ta kai ta adadin kudi Euro fiye da miliyan dubu biyu. A yan watannin da suka wuce kuma, gidan television na Bloomberg ya gabatar da rahoto game da dimbin dukiyar da iyalan Xi Jinping, wanda shine ake sa ran zai gaji shugaban kasa, Hu Jintao suke mallaka. A kasar ta China dai, manyan shugabannin siyasa ne suka mamaye harkokin kasuwanci, musamman tattare da manyan masana'antu da kamfanonin kasa. Umaru Aliyu ya rubuta wannan rahoto game da yadda manyan yan siyasar kasar ta China suka mamaye harkokin tattalin arzikinta.
A kasar ta China ba wani boyayyen abu bane sanin cewar manyan yan siyasa da shugabannin jam'iya sune suka mamaye aiyukan manyan kamfanoni da masana'antunta. Alal misali, wani dan taxi a garin Shijiazhuang dake wucewa ta kusa da wata katuwar tashar karfin lantarki mai amfani da kwal, ya shaidawa fasinjoji dake tare dashi cewar wannan kamfani ne mallakar iyalin Li Peng, wanda ya rike mukamin Pirayim minista har zuwa shekara ta 1998 a China.
A kasar dai babu wanda yafi amfana da bunkasar tattalin arziki da kasar tayi shekara da shekaru tana samu fiye da manyan shugabanni da masu mulki tare da iyalansu, saboda a garesu, akwai hanyoyi masu tarin yawa na maida kansu masu arziki cikin dare daya. Daya daga cikin wadannan hanyoyi da alamu ta samu, a lokacin da kasar ta tsunduma ga matakan sayar da hannayen jarin kamfanoni da masana'antun hukuma ga yan kasuwa masu zaman kansu a shekaru na casa'in. Gu Xuewu, masanin al'amuran siyasa a jami'ar Bonn dake nan Jamus yake cewa:
"Shekaru 10 zuwa 15 baya, an sayar da kamfanoni da masana'antun gwamnati masu yawa ga mutanen dake kan mulki ko mukarrabansu da magoya bayansu, tare da farashin da bai taka kara ya karya ba, abin da kusan ace sun kwace wadannan kamfanonmi da masana'antune ba tareda sun biya komai ba. Wadannan manyan yan siyasa da masu mulki sun tara dimbin dukiyarsu ne ba ta hanyar sayen hannayen jari a kasuwannin hada hadar kuidi ba, amma sai ta harkokin kasuwanci a kamfanonin da suka karabrwa kansu, ko sayen hannayen jari a kamfanoni ko masana'antu masu yawa."
Shugabannin basu tsaya kawai ga sayen hannayen jari a tsoffin kamfanoni ko masana'antun da gwamnati ta sayar ba. Iyalai da abokan wadannan masu iko, suna kuma zuba jari a harkokin kasuwanci masu zaman kansu, inda akan basu manyan mukamai tare da riba mai yawa. Jaridar New York Times alal misali, ta gabatar da rahoto a game da dan Wen Jiabao, wanda cikin harkokin sa na kasuwanci har da wani kamfani na tufafin wasanni da ya zuba jari a ciki, yayin da dan tsohon Pirimiya Zhu Rongji yake shugabantar bankin zuba jari mafi girma a kasar ta China. Jaridar tace manyan shugabanin na China suna da hannun su a kusan dukkanin fannonin tattalin arzikin China, yayin da masanin siyasa Gu Xuewu yace sauran kamfanoni ko masana'antun da gwamnati bata sayar dasu ba, tuni suka kasance sai yadda shugabanin suka yi dasu.
"Shugabannin siyasa da iyalansu sun tarawa kansu dimbin arziki ne saboda iyalai da danginsu gaba daya, tun daga yaya har zuwa ga jikoki duk sun kasance rike da manyan mukamai a kamfanoni da masana'antun gwamnati. A dukkanin kamfanoni da masana'antu 134 dake karkashin kulawar gwamnatin tsakiya a Peking, za'a taras manajoji da shugabannin su kai tsaye suka da dangantaka da masu mulki shugabannin jam'iya."
Wasu daga cikin kamfanoni na gwamnati a China ana iya jefa su a jerin wadanda suka fi girma a duniya, inda duk mai shugabanci su, dukiya har sai yaji baya so. Wani rahoto da cibiyar Wikileaks ta gabatar ya nuna cewar iyalan Li Peng sune masu mallakar bangaren makamashi, yayin da iyalan Zho Yangkang, wanda shine shugaban hukumar leken asirin China suke mallakar bangaren man fetur a kasar, ita kuma uwargidan Wen Jiabao ta mamaye masana'antun sarrafa duwatsu masu daraja a wannan kasa.
Mawallafi: Umaru Aliyu
Edita: Halima Balaraba Abbas