Shugabannin duniya na taya Trump murnar lashe zabe
November 7, 2024Zababben shugaban kasar Amurka Donald Trump na jam'iyyar Republicans ya samu sakwannin taya murna daga shugabannin kasashen waje, kama daga Emmanuel Macron na Faransa zuwa Benjamin Netanyahu na Isra'Ila da Volodymyr Zelensky na Ukraine da firaministan Burtaniya Keir Starmer da shugabar hukumar zartarwa ta kungiyar Tarayyar Turai Ursula von der Leyen. A nasa bangare, shugaban gwamnatin Jamus Olaf Scholz ya aika da sakon taya murna ga Donald Trump, yana mai tabbatar da cewa zai yi aiki da zababben shugaban Amurka "don inganta wadata da 'yanci". Scholz ya yi amfani da kafar X wajen bayyana cewar "Jamus da Amurka suna da dogon tarihi da nasara na yin aiki tare."
Karin bayani: Me zaben Amurka ke nufi ga Afirka?
Sai dai Rasha ta bayyana cewa shugaba Vladimir Putin bai shirya taya Trump murna ba, amma za ta yi aiki , ba tare da ci gaba da yaki a Ukraine. Saboda haka, fadar mulki ta Kremlin ta ce ba za ta yi sauran yanke hukunci kan alkiblar zababben shugaban kasar Amurka ba. Amma a bangarensa, Shugaban kasar Ukraine Volodymyr Zelensky ya taya Donald Trump murnar nasarar da ya samu, ya kuma ce yana fatan zai taimaka wa Ukraine wajen samun zaman lafiya. Shi kuwa shugaban kasar Turkiyya Recep Tayyip Erdogan ya yi maraba da nasarar Donald Trump da ya danganta da abokinsa, inda ya ce "Muna fatan dangantakar da ke tsakanin Turkiyya da Amurka za ta karfafa kuma yake-yake na duniya, musamman rikicin Falasdinu da yakin da ke tsakanin Rasha da Ukraine, za su kare."
Karin bayani: Ya ya ake zaben shugaban kasa a Amurka?
Gwamnatin Taliban a Afghanistan na fatan samun "sabon babin dangantaka" bayan sake zaben Donald Trump a matsayin shugaban kasar Amurka, wanda ya rattaba hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya da Taliban a wa'adinsa na farko. Kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Abdul Qahar Balkhi ya bayyana a shafin X cewar yana fatan samun ci-gaba mai ma'ana a dangantakar da ke tsakaninsu. Firaministan Iraki, Mohamed Chia al-Soudani,ya ce a shirye yake ya karfafa dangantakar kasarsa da Washington bisa shardin mutunta juna da cin moriyar juna. Shi ma shugaban kasar Iraki Abdel Latif Rachid yana fatan sabuwar gwamnatin Amurka za ta karfafa zaman lafiya da tattaunawa mai ma'ana a yankin Gulf. Da ma, gwamnatin Bagadaza na daukar matakan daidaita al'amura na nesanta Iraki daga rikicin yankin gabas ta tsakiya, kama daga na Zirin Gaza Hamas har i zuwa na Isra'ila da Hezbollah.
Karin bayani: Tasirin da sakamakon zaben Amurka ga kasar Jamus
Kamala Harris da ke zama mataimakiyar shugaban kasar Amurka mai shekaru 60 ta sha kaye, idan aka yi la'akari da jihohin da suka fada hannun Donald Trump mai shekaru 78 da haihuwa. Trump ya samu nasara a jihohin Georgia da North Carolina da Pennsylvania da ke cikin jerin jihohi bakwai masu muhimmanci wajen lashe zaben shugabancin Amurka. Tuni dai, Donald Trump ya samu manyan masu zabe 277 da ake bukata wajen samun nasara, yayin da Kamala Harris ta samu kasa da wannan adadi. Shi dai Donald Trump ya gudanar da yakin neman zabensa na uku a yanayi na yunkuri biyu na neman kashe shi, da kuma tuhume-tuhume hudu na aikata manyan laifuka. Yanzu haka dai, jam'iyyarsa ta Republican ta samu rinjaye a majalisar dattawan Amurka, baya ga na wakilai.