1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shugabannin duniya sun fara halartar taron G20

November 22, 2025

Taron G20 da za a gudanar da shi a karon farko a nahiyar Afirka, ba zai samu halartar shugabannin Amurka da Rasha da kuma China ba.

Shugabannin duniya sun fara halartar taron G20 a kasar Afirka ta Kudu
Shugabannin duniya sun fara halartar taron G20 a kasar Afirka ta KuduHoto: Kyodo News/IMAGO

Za a gudanar da taron koli na kungiyar kasashe 20 masu karfin tattalin arziki ta G20 a birnin Johannesburg na kasar Afirka ta Kudu. Sai dai shugaban Amurka, Donald Trump da kuma takwarorinsa na Rasha da China na daga cikin wadanda da ba za su samu halartar taron ba da ke gudana a karon farko a nahiyar Afirka.

Karin bayani:Kasashen G20 za su gana kan harajin Trump

Mai masaukin baki, Shugaba Cyril Ramaphosa na son taron ya mayar da hankali kan hadin kai da daidaito da kuma dorewarsu. A gefe guda, sakataren Majalisar Dinkin Duniya, António Guterres ya yi kira ga kasashe mambobin G20 da su yi amfani da tasirinsu da kuma muryoyinsu wajen kawo karshen rikice-rikicen da ke sanadin rayukan mutane a sassan duniya. Ana dai sa ran muhawara kan kwaryakwaryar daftarin kawo karshen yakin Ukraine da Amurka ta gabatar ya mamaye zauren taron.

 

Tsallake zuwa bangare na gaba Babban labarin DW

Babban labarin DW

Tsallake zuwa bangare na gaba Karin labarai daga DW