1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shugabannin ECOWAS na ganawa a Ghana

February 3, 2022

Juyen-juyen mulki a kasashen yammacin Afirka, ya sanya shugabnnin yanke sake haduwa a Ghana da nufin nazarin karuwar take-taken sojoji a kan gwamnatocin yankin.

Ghana Accra | Economic Community of West African States | ECOWAS
Hoto: IVORY COAST PRESIDENTIAL PRESS SERVICE/REUTERS

Shugabannin kasashen yammacin Afirka, sun fara wani muhimmin taro a wannan Alhamis a Accra babban birnin kasar Ghana, inda za su yi nazari a kan sabon juyin mulki da aka yi a yankin.

A ranar 24 ga watan jiya ne sojoji suka kwace iko a Burkina Faso, kasa ta uku ke nan da sojojin ke hambare shuganninsu cikin kasa da shekaru biyu.

Kafin Burkina Faso dai sun rusa dimukuradiyyar kasar Mali cikin watan Agustan 2020, sannan suka kifar da Alpha Condé a Guinea Conakry cikin watan Satumbar bara.

Rudani na baya-bayan nan ma da shugabannin na yammacin Afirka suka shiga, shi ne na harin manyan bindigogi da aka kai fadar shugaban kasar Guinea-Bissau, inda Shugaba Umaro Sissoco Embalo, ya tsallake rijiya da baya a ranar Talatar da ta gabata.

Tuni ma dai kungiyar ECOWAS ta kakaba takunkuman tattalin arziki a kan kasahsen Mali da Guinea, saboda kwace iko da sojojin suka yi.