EU na taro kan makomar Birtaniya
October 17, 2018Talla
Shugabannin na EU sun yi kalamai mabambamta lokacin da suke isa wajen taron na Brussels. A cewar Sebastian Kurz shugaban gwamnatin Ostiriya ba sa tsammanin cimma wata gagarumar nasara sai dai 'yan makonni ko watanni da ke tafe. Ita kuwa Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel cewa ta yi Jamus na cikin shiri ko da an gaza cimma yarjejeniyar da Birtaniya.
Ita kuwa Firaministar ta Birtaniya ta fada wa manema labarai cewa cike take da fata na cimma wasu matakai ga batun na ficewar kasarta daga EU da ma hulda da za su kulla. A cewar May batun da ake takaddama a kansa na iyakar Ireland za su tabo shi inda kuma take da fata za su cimma matsaya.