Za mu ciyar da EU gaba inji Merkel
September 16, 2016Shugabannin kasashen kungiyar tarayyar Turai a karshen taron kolin da suka gudanar a Bratislava babban birnin kasar Slovakia sun amince da sabuwar taswira da za ta ciyar da kungiyar gaba.
Taswirar dai ta kunshi hanyoyi da kuma dabarun inganta amincin al'umma da kuma yarda a tsakanin kasashen kungiyar bayan sakamakon ba zata na kuri'ar raba gardamar da Birtaniya ta kada na ficewa daga kungiyar.
Jakadu a taron sun ce tattaunawar ta gudana cikin nasara.Kasashen sun jaddada kudirin yaki da ta'addanci don tabbatar da tsaron nahiyar Turai.
Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel ta yi tsokaci:
" Ta ce kada yi tsammanin a taro guda za'a warware dukkan matsalolin nahiyar Turai. Muna cikin wani yanayi na tsaka mai wuya, to amma wannan dama ce ta nuna cewa ta hanyar daukar mataki, za mu iya inganta lamura musamman ta fuskar tsaro a cikin gida da waje da kuma yaki da ta'addanci."