Shugabannin EU zasu ɗauki guda kan batun Kosovo
December 14, 2007Talla
A taron ƙolin da suka yi a birnin Brussels shugabannin ƙungiyar tarayyar Turai EU sun ƙuduri aniyar cimma matsaya ta bai ɗaya a dangane da batun ´yancin kan lardin Kosovo. A cikin daftarin sanarwar bayan taro ƙungiyar ta EU ta ce zata taka muhimmiyar rawa a wannan batu. To sai dai ba a ambaci kalmar ´yanci kai a cikin daftarin sanarwar bayan taron ba. Kasashen Cyprus da Slovanyia da Girika na ƙin duk wata shailar ´yancin kai da Kosovo zata yi daga tarayyar Sabiya. SGJ Angela Merkel ta yi kira da a samu matsayin daya dangane da wannan batu.