Shugabannin Igbo sun cimma matsaya kan Biafra
July 3, 2017Daukacin shugabannin a yankin na Kudu maso Gabashin na Najeriya, yankin kuma da ya sa rajin san ballewa daga tarayyar ta Najeriya a gaba tsawon lokaci, sun kammala taron nasu ne a daren jiya Lahadi, inda gwamnoninsu biyar da sanatoci da kuma 'yan majalisar kasa masu ci, da babbar kungiyar hada kan 'yan kabilar Igbo ta Ohaneze Ndigbo da sauransu, inda kuma suka cimma matsayar cewar daga yanzu ba batun raji da kwayayaton son kafa Biafra a yankinnasu illa dai a dubi alkiblar tabbatar da Najeriya a kasa daya al'umma daya.
To sai dai kuma cimma hakan na cewar yankin na Igbo zai dena bada kafar ci gaba da rajin ballewa daga tarayyar ta Najeriya inji wadannan shugabanni na kabilar ta Igbo, ya zama dole a sake fasalta zamantakewa a kasar ta Najeriya, da hakan ke nufin dubi ga yanayin siyasa da tattalin arziki don aiwatar da gyara a kai, sannan kuma suka ce dole a sake duba kundin da ke kunshe da tanade-tanade kan taron kasa da aka gudanar a shekara ta 2014 zamanin tsohon shugaba Dr. Goodluck Jonathan don aiki da su a kasar. Haka kuma taron na Igbo da aka gudanar a birnin Enugu ya yi Allah wadai da furucin kin jinin juna a kasar.
Yanzu dai halin da ake ciki shi ne cewar shugabannin na kabilar ta Igbo sun ce za su kafa wata majalisa mai karfi a yankunnasu da za ta rika magana da yawun daukacin yankin na Igbo da nufin tabbatar da cimma burinsu na tabbatar da gaskiya da adalci ga yankinsu da ma kowane sashe na Najeriyar.
Sai dai kuma yayin da shugabannin na Igbo ke batun cimma wannan matsaya na rungumar Tarayyar Najeriya akwai rarrabuwar ra'ayoyi na 'yan kabilar ta Igbo kan hakan, inda bayan masu tsaka tsakin ra'ayoyi, su kuma masu rajin son kafa Kasar ta Biafra sun fi yawa nesa ba kusa ba, tare da cewar matsayar da shugabannin na Igbo suka cimma ba da yawunsu ba.